Labarin wata matashiya ya jawo ce kuce a kafafen sada zumunta na zamani inda budurwar ta aure mahaifin tsohon saurayin ta dan kimanin shekaru 89.
Matashiyar dai ta bayyana dalilin da yasa ta auri mahaifin tsohon saurayin na ta inda ta ce tsohon saurayin na ta yaci amanar ta ne. Ita kuma taga ba za ta iya cigaba da rayuwa dashi ba hakan ne yasa ta koma soyyaya da mahaifinsa har suka yi aure.
Sai dai budurwar ta sha tsokaci inda wasu ke kiran ta suna zagin ta, wasu kuwa suna yi mata martani na kalamai mara dadi. Wanda hakan ya harkuta ita ma ta fito ta mayar da martani aka masu zagin ta.
Inda tace su mutane ba su dubi abinda tsohon saurayin na ta yai mata ba na cin amana inda ya dinga bin kawayen ta yana cin amanar ta. Tace meysa shi ba'a ga laifin sa ba sai ni da na auri mahaifin sa.
Tace ita aure tayi na soyyaya kuma babu wanda ya isa ya raba ta da mijin ta. Don haka duk wanda yake ganin cewa naci amana ne to sai kuyi ta yi.