Yadda Aka Kame Wani ƙasurgumin Ɗan Bindiga Da Ya Jima Yana Addabar Kaduna


A safiyar Asabar, wato ranar sallah rundunar Yan sandan Kaduna ta yi nasar kama wani ɗan kungiyar "Fulani Bandits" da bindiga da albarusai masu yawa yayin wani wani harin taadancin da ya kai. 


An kuma tabbatar cewa yana daga cikin yaran Nasiru Kachalla, wato kasurgumin dan ta'addan nan da ya addabi yankin Kaduna da Neja. 


Bugu da ƙari, rundunar ta ce matashin mai suna Manu Bello ya amsa zargin da ake masa na ta'adanci tare da kashe al'umma da sace dukiyoyi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post