Wata Ala'da Da Ake Warewa Budurwa Daki Tana Kwanciya Da Samari Har Sai Taji Wanda Yai Mata Sannan A Daura Musu Aure


Al'adu na ban mamaki a duniya basa karewa, kusan ko da yaushe zaka ji irin wasu al'adun mutane wanda sai ka dauka cewa ba su da hankali ne amma kuma ba rashin hankali bane kawai al'adar su ce haka. 


Ko a kwanakin baya mun kawo muku labarin wata kabila a yankin Kudancin Afrika wanda idan budurwa za ta yi aure kafin ta tare da mijin ta sai mijin ya fara kwanciya da Antin amarya domin a jarraba lafiyar sa sannan sai ya tare da amarya. 


Sai dai mu a Najeriya musamman inda musulunci yai tasiri da wuya kaji irin wasu al'adu irin wanda suke da iri daya da wanda ba na musulmai ba. 


A kasar musulmi za ka samu budurwa tana kare kanta da mutuncin ta daga gun dukkan wanda ba muharammin ta bane. Kuma zaka same su da shiga mai kyau da kamala. 


Sai dai al'adar wata kasa da ake kira da Cambodia su al'amarin nasu ba haka yake ba, domin duk budurwa kafin ta yi aure sai anyi mata daki wanda za ta dinga kwanciya da samari har sai ta samu wanda ya iya gamsar da ita. 


Da zarar yarinya ta kai shekaru 16 'yan uwanta za su gina mata daki a kusa da gidan su wanda za ta dinga tara samari suna kwanciya da ita suna kwana tare, duk wanda ta samu yai mata to shi za ta zaba a matsayin wanda za'ayi musu aure. 


Sai dai idan ta fitar da mijin idan aka daura musu aure to babu abinda zai raba su sai dai mutuwa. Hakan yasa suke gudanar da wannan al'adar ta su. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post