Demi Minor an dauke shi daga cikin fursuna mata inda aka mayar dashi cikin Kurkukun maza biyo bayan samun sa da aka yi yaiwa wasu fursunoni mata 2 ciki a Kurkukun mata dake New Jersey ta Amurka.
A rahoton da Daily Nigerian ta wallafa ta rawaito cewa Minor an yanke masa zaman shekaru 30 ne a zaman gidan yari biyo bayan kashe mutumin da ya raine shi a matsayin uba. An dauke ta daga gidan gyaran hali na Edna Mahan zuwa gidan gyaran hali na matasa na jihar a watan Yuni.
Ana tsare da ita a wani waje mafi kazanta a gidan yarin.
Matashiyar mai shekaru 27 da haihuwa, ta koka da yadda masu gadi suka yi mata ba daidai ba da cin zarafi a lokacin canja gidan yarin, har ma an sanya ta a cikin fursunonin da a ke sa musu idanun don kada su kashe kansu bayan ta yi kokarin rataye kanta a lokacin da ake kai ta GSCF.
A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Justice 4 Demi, Minor ta yi ikirarin cewa jami’an gidan yarin na fakon ta, inda daya daga cikinsu ya yi mata ba’a a lokacin da a ka ce a tube mata kaya domin bincikar ta.
A wani rubutu na daban, ta yi zargin cewa an yi mata dukan tsiya a lokacin canja mata gidan yarin.