Adam Muhammad, wani mahajjaci ne dan kasar Iraqi, wanda ya isa birnin Makkah da kafarsa, inda ya ratsa kasashe kusan 11 yana tafiya, ya kuma kwashe kusan watanni 11 yana tafiya domin isa kasa mai tsarkin don sauke farali a bana.
Adam Muhd dai ya dade yana mafarkin ganin yaje kasa mai tsarkin a kafa, abun da mutane da dama suke ganin ba abu bane mai yiwuwa kasancewarsa mazaunin kasar Burtaniya, yace bayan ya isa birnin Makkah, ya yi umrah, ya kuma shafe lokaci mai tsawo a Ka’aba mai alfarma.
Mahajjacin, wanda ya shafe kimanin shekaru 25 yana zaune a kasar Biritaniya, ya yi mafarkin yin tafiya ta ibada zuwa saudiyya ne domin gudanar da aikin Hajji wanda guda ne cikin shika-shikan addinin musulunci, Amma mafarki na gaske shine da ya fara tunanin zuwa kasar saudiyyar da kafafunsa.
Ya kara dankon cewa tun lokacin da aka sanya dokar hana fita bayan barkewar cutar corona, na shagaltu da karatu da fahimtar ma’anar Alkur’ani mai girma. Kuma bayan shekara daya da rabi na zurfafa nazari Cikin Littafi Mai Tsarki, sai na farka daga barci wata rana da wata dabara ta cewa kawai in tafi Makkah da kafata mana.
Adam dai ya taso ne daga kasar Biritaniya a ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2021, inda ya nufi Makkah domin gudanar da aikin Hajji, dauke da kayan sa. Mahajjacin mai shekaru 52 a duniya ya ce ya dauki watanni biyu kacal a shirye-shiryensa na zuwa aikin hajji, kuma wata kungiya ta Biritaniya ta bashi taimako. Dangane da wannan tafiyar mai cike da kalubale da ya kudirci aniyar yi, amma Adamu ya ce bai fuskanci wata babbar matsala ba a hanyarsa ta zuwa Makka.
“Babu wata babbar matsala illa tsarewar da hukumomin ‘yan sanda suka yi min a kasashe da dama domin su tambaye ni daga inda na ke, amma duk sun yi mamakin jin kudirina na musamman da Basu taba ji ba wato zuwa Makkah a kasa.
“Mutane da yawa sun taimaka min a lokacin da nake kan hanyata, amma ban taba neman taimako daga kowa ba,” in ji shi yayin da yake jaddada cewa abin da yake yi don Allah ne ba don wani abu ba.
Da yawa daga cikin mazauna garin Makkah da mahajjata da suka halarci masallacin nana A’isha da ke Al-Taneem sun bayyana jin dadinsu da zuwan Adam, wanda ya fara tattaki da kafarsa daga kasar Birtaniya cikin watanni 10 da kwanaki 25 da suka wuce, inda ya ratsa kasashe 11.
Adam ya godewa al’ummar Saudiyya da suka karama sh tun lokacin da ya Isa kasar ta saudiyya, A yanzu haka dai Adam ya shagaltu sosai da shirye-shiryen ganin ya gudanar da aikin Hajji wanda za’a gabatar nan da kasa da mako guda.