Dakarun Sojojin Nijeriya na Operation Desert Sanity Dakarun sun kashe 'yan ta'addan ISWAP da Boko Haram da dama ciki har da manyan kwamandojin su a wani samame da suka kai a hanyar Dikwa zuwa Gamboru a jihar Borno.
An kuma yi nasarar kama makamai da alburusai da dama a yayin kai harin.
A ranar alhamis bakwai ga wafan Yuli ne rundunar sojin suka yi nasarar kashe ‘yan ta’ddan a sabon harin da suka kai masu kamar yadda suka bayyana a shafukansu na sada zumunta.
Kuma sun kai masu harin ne yankin babbar hanyar Dikwa Gamboro, yayin suka kara da cewa sun dakko manya manyan makamai ‘yan ta’addan.
Daga Aliyu Samba