Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya Baiwa Ministan Ilimi Mako 2 Domin A Karshen Yajin Aikin ASSU - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Shugaban kasa Muhammadu Buhari Ya Baiwa Ministan Ilimi Mako 2 Domin A Karshen Yajin Aikin ASSU


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bawa Ministan ilimi Adamu Adamu tsawon makonni 2 domin kawo karshen yajin aikin ASUU da aka shafe kusan watanni 7 ana yi. 


Sanarwar ta shugaban kasa ta fito ne tun ranar Talata inda ya bayar da umarni ga Ministan ilimi cewa a zauna da malaman Jami'a a sasanta da su akan abubuwan da ake takaddama dasu. 


A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya samu ganawa da wasu masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi na kasar wanda ake tunanin zasu iya kawo karshen matsalar. 


Rahoton ya bayyana cewa Shugaban kasar ya kira su ne domin ya samu karin bayani a kan dalilin da ya sa wannan yajin aikin yaki ci yaki cinyewa.


Yanzu abin jira a gani shine Ko nan da sati 2 za'a samu kawo karshen wannan yajin aikin da aka dade ana yi? Lokaci ne dai zai tabbatar mana da hakan. 

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel