Daya daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok da ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace a ranar 14 ga watan Afrilun 2014, ta tsallake rijiya da baya a dajin Sambisa.
Ƴan ta’addan sun kai farmaki a makarantar sakandiren ƴan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno inda suka yi awon gaba da ƴan mata sama da 250 da ke rubuta jarabawar karshe a lokacin.
Bayan ta tsere daga yankin ƴan ta’addan a jihar Borno, daga karshe sojojin Najeriya sun gano ta a ranar 29 ga watan Yuni. Bayan kwana biyu ta yi jawabi ga ƴan jarida inda ta ba da labarin irin halin da ta shiga a hannun ƴan ta’addan.
Matar wadda ta bayyana sunanta da Ruth Bitrus, ta ce sai da ta yi tattaki na tsawon kwanaki uku a cikin dajin Sambisa kafin daga bisani sojojin runduna ta 21 da ke Bama masu sulke suka zo mata.
“Sunana Ruth Bitrus, na tsere daga dajin Sambisa. Ina daya daga cikin daliban da aka sace daga GGSS Chibok a watan Afrilun 2014. Mu 203 ne aka sace. Har yanzu sauran mu muna Sambisa tare da wadanda suka yi garkuwa da mu,” ta yi bayani a harshen Hausa.
A cewar Ruth, an kashe mijinta ne ta hanyar fashewar wani abu a lokacin da yake kokarin tayar da bam.
“Mahaifin yarona ya rasu ne shekaru biyu da suka gabata a kauyen Rabul Sani inda ya je ya dasa bam a wajen aikin soja kuma ya fashe da shi kafin ya dasa shi.”
Mahaifiyar a cikin damuwa ta bayyana cewa ta dauki abinci da ita wanda ta yi amfani da ita wajen ciyar da yaron a cikin kwanakin ukun.
Ceto Bitrus ya zo ne makonni biyu bayan da sojoji suka ceto wasu ‘yan matan makarantar Chibok biyu – Mary Dauda da Hauwa Joseph – bayan da suka tsere daga sansanin Gazuwa da ke da nisan kilomita tara zuwa karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Kubucewar nasu ya biyo bayan wani gagarumin farmaki da dakarun Operation Hadin Kai suka kai musu, wanda ya kai ga yunwa da kaura a yankunan ƴan ta’addan.
A cikin sama da ‘yan mata ‘yan makaranta 200 da ‘yan ta’addan suka sace a shekarar 2014, sama da 100 daga cikinsu ba a san duriyarsu ba tsawon shekaru takwas bayan sace su.