Na haife santalelen yaro ba tare da na Sadu da wani namiji ba


Wata mata ƴar ƙasar Ghana mai suna Aba, tayi iƙirarin cewa ta samu juna biyu sannan ta haihu ba tare da ta sadu da namiji ba.


Matar ta bayyana cewa shekarar ta huɗu rabon da ta sadu da wani namiji. Da take magana a wata hira da Barima Kaakyire Agyemang a tashar Step 1 TV, Aba tayi iƙirarin cewa bata sadu da wani namiji a tsawon shekaru huɗu da suka wuce ba.


A cewar ta, lokacin da ta fara jin wani baƙon ciwon ciki da kumburi, ta ɗauka cewa ‘fibroid’ (ƙarin mahaifa) ne. Bayan taje asibiti, ta bayyana cewa likitoci sun shaida mata cewa tana bukatar ayi mata tiyata domin a cire shi.


Ta ƙara da cewa ta ji bukatar ta turo ƙarin mahaifar ɗin waje saboda hana yi mata tiyata a ciro shi, a mamakin ta, kawai sai jaririn yaro ya sulluɓo.


Ta bayyana cewa tana buƙatar taimako wajen ɗaukar ɗawainiyar yaron. Matar wacce yanzu ta zama sabuwar uwa tana sayar da ruwa a bakin titi, ta kuma bayyana cewa bata da halin da zata ɗauki dawainiyar yaron. Ta kuma bayyyana cewa wata matar wani fasto ce take ɗaukar ɗawainiyar ta da ta jaririn kaɗan-kaɗan yadda zata iya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post