Jarumar Da Za Ta Maye Gurbin Sumayya A Cikin Shirin Labarina


Fitacciyar jarumar masana’antar shirin fina-finan ne kannywood wato, Habiba Aliyu wanda akafi sanin da ummi Alaqa bisa alamu itace zata maye gurbin Nafisa Abdullahi (Sumayya) a cikin shirin ne mai dogon zango na LABARINA SERIES.


Biyo bayan saɓanin da aka samu tsakanin darakta Aminu Saira da Nafisa Abdullahi wanda yasa aka cire ta daga cikin shirin. Kuma tun bayan lokacin ne dai ba'a cigaba da haska shirin ba.


jaruma Ummi Alaqa ta wallafa a shafinta na Instagram bayan ta hada hotunan da na Nafisa Abdullahi daga nan tace.


Nan da nan mutane suka bazama suna ta tsokaci karkashin wallafar, wasu suna ganin zata taka babbar rawa, yayin da wasu suke ganin Gogewarta bata kai ta maye gurbin Nafisa Abdullahi wato Sumayya ba.


Yanzu dai abin jira agani shine ko wannan hasashen zai tabbata? kuma idan ya tabbata shirin zai cigaba da yin armashi kamar yadda ake gudanar dashi tun a baya? Lokaci ne dai kaɗai zai iya tabbatar da hakan. kucigaba da kasancewa damu domin kawo muku halin da ake ciki.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post