Wani rahoto dake yawo a kafafen sada zumunta a Najeriya na nuna cewa aƙalla gidajen burodi 40 ne suka rufe suka daina sarrafa shi a babban birnin tarayya Abuja, a sakamakon tsadar farashin kayayyakin aiki da kuma ƙarin haraji da kuɗin wutar lantarki da dai sauransu.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, wasu gidajen biredi da aka ziyarta ba a buɗe su ba saboda basa yin aikin a dalilin tsadar kayan haɗa shi da kuma haraji da wasu hukumomin gwamnati ke karawa.
Wasu daga cikin gidajen burodin da suka rufe shago sun haɗa da Abumme bakery Ltd. Lugbe, titin Airports, Hamdala Bakery, Kuje, Harmony Bite Bakery, Karu, Doweey Delight Bakery Ltd, Kubwa.
Sauran sun hada da Merit Baker, Mpape, Funez Baker, Orozo, Slyz Bakery, Wuse Zone 2, da sauransu.
Ishaq Abdulraheem, Shugaban Kamfanin Biredi na Abuja Master Bakers, FCT, ya bayyana cewa abin damuwa ne ganin cewa gidajen burodin da ke Abuja ba za su iya jurewa tsadar kayan aiki ba.
Ya ce akasarin ‘yan kungiyar sun rasa abin yi, yayin da ma’aikata ma sun rasa aikin yi saboda rufe gidajen burodin da a ka yi. Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta shiga tsakani, ta kuma duba hukumomin gwamnati da ke kawo cikas ga harkokin kasuwancin biredi.