Gwamnan Kano Ganduje Yai Afuwa Ga Mutane 13 Da Aka Yanke Musu Hukuncin Kisa - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Gwamnan Kano Ganduje Yai Afuwa Ga Mutane 13 Da Aka Yanke Musu Hukuncin Kisa


Gidan talabijin na Artv Kano ya rawaito cewa, gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje tayi afuwa ga fursunoni 90 daga gidan yari cikin su har da wasu 13 da suke jiran hukuncin kisa.


Gwamnan ya aiwatar da hakan ne sakamakon bikin Babbar Sallah. Dama kusan duk shekara yakan yi hakan, amma dai na bana yazo da mamaki tunda bai taba yin afuwa ga waÉ—anda aka yankewa hukuncin kisa ba.


A wata sanarwa da mai magana da yawun gidan gyaran hali na Najeriya reshen Jihar Kano Musbahu Lawan K Nassarawa ya saka wa hannu, gwamnan ya biya wa mutum 77 diyyar kuÉ—in da ake binsu domin fita daga gidan gyaran halin haka kuma akwai mutum 13 da aka yanke wa hukuncin kisa a baya da halayansu aka gamsu da su wanda hakan ya sa gwamnan ya yi musu afuwa.


Haka kuma akwai fursunoni uku da aka yanke wa hukuncin kisa da gwamnan ya yi musu afuwa aka mayar da hukuncinsu É—aurin rai da rai.


Haka kuma Gwamna Ganduje ya kuma bai wa fursunonin shanu da raguna da shinkafa domin su ji daÉ—in Babbar Sallah.

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel