Falalar Allah tana da yawa ga bayinsa, sabo da haka ne Allah ya tattalarwa bayinsa lokuta na musamman don yawaita ayyukan alhairi, suna rige-rige a cikinsu, suna neman kusanci zuwa ga ubangijin su.
Ranar Arfa daya ce daga cikin ranku na musamman mai girman falala, rana ce da Allah ya kebe ga bayinsa, musamman don lada garabasa mai yawa, da kankare zunubbai, da afuwa, da saukar da rahama da gafara, da ‘yanci daga wuta.
Ranar Arfa ita ce ranar Tara ga watan Dhul-Hijjah, wanda mahajjata suke tsayuwa a farfajiyar Arafa na garin Makka, suna Ambaton Allah, sauran al-uma kuma suna azumi da sauran ibadu. Ranar da take tunatar da musulmi tsayuwan kiyama. Bayin Allah sukan tsayu a gaban ubangijinsu a matsayin bayi cikin tufafi iri daya, dai-dai da dai-dai, babu bambanci tsakanin shugaba da mabiyi, mai-mulki da talaka, mawadaci da talaka, fari da baki, babu wani bambanci tsakaninsu, babba ko yaro, mace ko na miji, duk sun shagala cikin ganawa da ubangiji, suna ambatonsa, suna neman gafararsa da yardansa.
FALALAR RANAR ARAFA
1. Rana ce da addinin musulunci ya kammala, musulmi sukayi aikin hajjin su na farko wanda rukunnan musulunci suka cika.
2. Rana ce da Allah ya cika ni’imarsa ga wannan al-uma.
3. Rana ce da Allah yayi rantsuwa da ita a cikin Al-kur’ani har guri biyu, kuama rantsuwar tana nuna muhimmancin ranar. (Al-Buruj:3, Alfajar:3).
4. Ranar Arfa rana ce daga cikin mafi darajar ranaku a gorin Allah a cikin wata mai alfarma.
5. A ranar Arfa Allah yana sakkowa sama ta farko kuma yayi alfahari da mutanen duniya.
6. Ita ce ranar da Allah yafi ‘yanta bayi daga wuta.
7. Ranar Arfa ce, ake kira YAWMUL HAJJUL AKBAR wato ranar hajji mafi girma, Kuma tsayuwar Arfa itace hajji inji manzon tsira (SAW).
8. Azumin ranar arafa yana kankare zunubin shekara biyu ga wanda ya azumce shi.
9. Rana ce na gafartawa da jinkai da rahama ga bayin Allah.
10. Rana ce da Allah yake kunyata shedan, ya wulakanta shi kuma ya tozarta shi.
11. Ita ce ranar da shedan ke shiga bakin cikin da bai taba shiga ba, bayan ranar Badar.
12. Rana ce da Allah ke biyan bukatun bayinsa kuma ya karbi addu’ar su.
13. Rana ce da Allah yayi alkawali da BANI ADAMU baki daya da su kadaita shi da ibada (Al-A’araf: 172)
ABINDA AKE BUKATAR MUSULMI YA YI A RANAR ARAFA
1. Tsayuwar arfa ga mai aikin Hajji.
2. Azumin ranar Arfa ga mazaunin gida.
3. Yawaita Istigifari da Tuba, duk musulmi ya tuba ga Allah tuba na gaskiya.
4. Nisantar Zunubai da miyagun aiyuka: bawa ya nisanci sabon Allah, sabon Allah da zunubi suna nisartar da bawa daga rahamar Allah da yafiyar sa. Sabon Allah a lokuta na mussaman ya fi girman zunubi
5. Yawaita Zikiri: kamar kabarbari, tahmidi da hailala, da sauran dukkanin ambaton Allah.
6. Kyautatawa marayu, makwabta, ‘yan-uwa da sauran al’uma.
7. Yawaita Addu’a ga kai, iyaye, iyalai, ‘yan-uwa musulmi da kasa.
8. An karbo Hadisi daga Ibni Abbas annabi SAW ya ce mafi alhairin addu’a ita ce
addu’a ranar arafa. Kuma mafi alhairin abinda nake fadi da sauran annabawan da suka gabace ne, shi ne:
لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد، وهو على كل شيء قدير
Allah muke roko da ya biya bukatunmu kuma ya azurtamu da Aljannar sa. Amin.