Labaran Kannywood
Duk Kudinka Wallahi Idan Baka Da Kyau Ba Zan Iya Auren Ka Ba, Inji Moofy (Mai Fassara Finafinan Algaita)
Tuesday, July 12, 2022
0
Wani batu da Moofy tai ya girgiza al'umma musamman masu bibiyar ta a kafafen sada zumunta na zamani.
Moofy ta bayyana cewa “Zan iya auran talaka kyakkyawa mu zauna cikin mutunta juna, ladabi, so da kuma kauna har abada, ya fi min salama da kwanciyar hankali”.
Amma duk kudin mutum indai mummuna ne to gaskiya babu ni babu shi, duk iya kwalliyar sa duk wani gayun sa indai bashida siffar kyau to babu ni babu shi.
Sai dai kuma wasu na ganin cewa tayi hakan ne cikin raha ba wai dagaske take ba. Amma dai alamun yadda tai furucin ne babu akamar wasa a tare da ita. Hakan yasa wasu ke cewa ba wasa take ba.
Daga Mutawakkil Gambo Doko
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment