Tun bayan da Jarumar cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango Rahama MK tayi aure a baya-bayan nan Jama’a suke tofa albarkacin bakin su akan auren da tayi, da kuma ganin a wani matsayi take akan cigaba da shirin Fim musamman shirin Kwana Casa’in mai dogon zango da ta saba fitowa.
Sai dai kuma a jawabin ta cikin wata hira da jaridar Damukaradiyya sukai da ita ta bayyana musu cewa ba za ta daina sana'ar film ba za ta cigaba da fitowa a ciki musamman a shirin Kwana Casa’in mai dogon zango Rahama wanda a shirin ne aka santa.
Jarumar ta kara bayyana cewa: Harkar fim kamar aikin Gwamnati ne ko kasuwanci da Matan aure suke yi, haka za ta cigaba da yin fim tun da sana’ar ta ce da take yi kuma take samun kudi saboda aure na ba zai hana ni fitowa a fim ba.