A wannan zamanin abu ne mai matukar wahala ka samu budurwa wacce za tace da saurayi 1 kawai take tare. Duka macen da ta faɗama saurayin ta hakan to karya takeyi ta fadamasa ne don dai ya kara yarda cewa shi kadai take kulawa.
Mata da yawa musamman ƴan mata wanda basu taba yin aure ba sukan so su tara masoya da yawa saboda wasu dalilai. Sai dai bayan binciken da muka gudanar mun gano wasu dalilai 5 da yasa mata suke yawan tara samari a wannan zamanin. Ga jerin dalilan kamar haka:
(1) Rashin Mafadi:
Tabbas rashin mafadi na daya daga cikin dalilin da yasa da yawan yanmata tara samari domin wata a ranta ga wanda take so kuma ya kawo kome gidansu amma tatara samari da yawa tana hira dasu kuma har ga Allah a ranta ba da niyyar yaudaraba, kuma hakan yana faruwa ne a sakamakon rashin mafadi. Idan mace tana da me fadamata taji da hakan bazai ma kusa da faruwa ba balle yafaru.
(2) Son Abun Duniya Da Ruwan Ido:
Wata macen masu tara samari zaka samu dama kwadayayyiya ce dan haka abun duniya take so ido rufe, hakan yasa sai tai ta tara samari suna kashe mata kudi. Wanda taga alamun yafi bude bakin aljihunsa koko taga alamun nasha nasha atare dashi. A haka za tai ta tara ku kamar takalma sai bayan ta gama bata muku lokaci sai ta koreku ko kuma kuji ansaka auren ta da wani daban.
Wata ita ba son abun duniya bane illa kawai ɗabi'ar tace haka ta kasa tsaida daya a ranta yau tace wancen yau tace wane zuciyarta takasa tsaida guda.
duk wanda yace yana sonta takan bashi damar zuwa gunta sai taga ba wata mamora sai ta koreshi idan kuma me abun duniya ne ita kuma din me matsanancin son abun duniya ce shike nan sai ta mai dashi atm card tai ta fidda kudi.
(3) Salon Yaudara
Wata saboda salon yaudarane kodai don ɗaukar fansa ko dan haka kawai ita dai tana so taga ana yimata layi tana gwara kan samari.
Inba dan yaudara ba kedai kinsan daya akace ki aura ba 2 ba to ina ke ina tara samari da yawa. Watafa tana da nata saurayin a gefe amma nan kuma tataraku a gefe tana batamuku lokaci. Idan bakin aljihunku ba a bude yake ba tai ta wanke ka.
(4) Rashin Samun Saurayi Tsayayye Wanda Ya Mallake Zuciyar Ta:
Idan yazama saurayi ya kasa mallake zuciyar budurwarsa to akwai yiwar da wani yazo takula shi har tatarasu da yawa daga nan kuma ta fidda gwaninta.
Amma matukar budurwar tasami wanda ya gama sace mata zuciya ai shikenan sam zataji batama kanta lokacine ma ta saurari wani saurayi da sunan soyayya tunda ga gwaninta.
(5) Tsoron Yaudara Da Wulaƙanta Samari:
Wasu yan matan suna da wannan tunanin marar kyau wai tsautsayi ne zama da saurayi daya, don haka sai su yi ta tara samarin dayawa. Mai dan tunani ce take tara samari kamar 2 ko 3 kowane daga cikinsu akwai ranar da zai zo, shima wannan salon Yaudara ne a fakaice.
Wannan sune dalilai 5 da muka binciko dake saka yan mata tara samari da yawa. Muna fatan masu yin wannan halin da suyi ƙoƙari su gayra domin ba abune mai kyau ba. Domin a irin tara samari da yawa ne wasu matan ake hure musu kunne har yakai daga baya kuma su zo suyi nadama.