Nura Mustapha Waye, Daraktan fim ɗin Hausa mai nisan zango, Izzar So ya rasu a safiyar Lahadi a birnin Kano.
Freedom Radio ta rawaito cewa Mustapha Waye ya rasu ne a mutuwar fuj'a, ana sa ran za'a yi jana'izarsa nan gaba a birnin Kano.
Sanarwar ta fito ne daga gidan jaridar Freedom Radio inda take cewa.
"Allah ya yiwa Nura Mustapha Waye Daraktan shirin Izzar So mai nisan zango rasuwa a safiyar yau Lahadi."
Rahotonni sun ce Mustapha Waye ya rasu a mutuwar fuj'a, ana sa ran za a yi jana'izarsa nan gaba a yau a birnin Kano.
Allah ya gafarta masa.