Wata Budurwa me suna miss siyama ta bayyana cewa da ta auri talaka gwara ta auri dan giya. Budurwar ta wallafa hakan ne a shafin ta na twitter wanda hakan ya nuna cewa idon ta ya riga ya rufe da san abin duniya.
Wanda kuma a yanzu zamanin da muke ciki yawancin yan mata sunfi son auren mai kudi akan talaka duk da cewa kuwa yawancin yan matan bawai Suna son masu kudin tsakani da Allah bane kawai dai suna son sune dan arzikin da Allah yayiwa masu.
Wannan firucin da matashiyar ta yi ya jawo hankalin mutane musamman a kafafen sadarwa na zamani inda ake ta yin tsokaci akan hakan.