Da Mutane Ne Suke Bayar Da Aljannah Da Ba Za Su Bawa 'Yan Film Ba, Cewar Hauwa Waraka


A wani shiri da gidan BBC Hausa suke yi na "Daga Bakin Mai Ita" a wannan makon sun karbi bakuncin fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood Hauwa Waraka. 


A cikin hirar jarumar ta bayar da takaitaccen tarihinta inda tace asalin sunan ta shine Hauwa Abubakar amma ana yi mata lakabi da Hauwa Waraka. Kuma ita 'yar asalin garin Jos ce amma a jihar Kano ta girma tai wayo. 


Sunan da ake yi mata lakabi dashi tace ta samo shi ne daga film din "Waraka". Wanda kuma daga bisani ta daina harkar film din har tsawon shekaru kafin ta kuma dawowa. 


Anyi mata tambaya akan mene dalilan da yasa take yawan fitowa a mutuniyar banza, inda ta bayyana cewa tana yin hakan ne domin fadakarwa ga masu irin wannan halayen. 


Sai dai tace mutane da dama suna yi mata kallon mutuniyar banza, wasu suna tunanin abubuwan da take yi a cikin film a zahiri ma haka take yi. Inda ta bayyana cewa ba ta jin dadi irin yadda mutane suke yi mata wannan kallon. 


Sai dai tacemin duk da wannan kallon da mutane suke yi mata hakan baya damun ta tunda ba sune suke da wuta da aljannah ba. 


“Na yarda da Allah, na yarda da mazonnin Allah, na yarda da sunnoninsa, na yarda da mala’ikunsa, na yarda da littafansa, kuma na yarda da ranar kiyama, kuma na yarda da kalmar La’ilaha illallahu Muhammadar rasulullahi sallallahu alaihi wa sallam.


“Kuma ni abinda nake gaya wa al’umma na san mutum dai bai da makullin wuta bai da makullin Aljanna. Balle yace ai nine mai makkulin wuta, wuta zan kai ka ko kuma nine mai makullin Aljanna, Aljanna zan kai ka.


“Domin yawancin mutane kallon da suke yi mana, inda su suke bada Aljanna, yawancin mutane ba za su ba dan fim ba. Magana ta gaskiya, saboda akwai mutanen da ko sunana aka kira, sai kaji sun ce wannan makamashin wutar? Ni kuma naga baka da wuta baka da Aljanna. Allah shi ke bada ita ba mutum ba.”

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post