Daga karshe dai ya tabbata Fati Washa itace ta maye gurbin Nafisa Abdullahi wato Sumayya a cikin shirin nan mai dogon Zango na "LABARINA".
An shafe tsawon watanni ba tare da cigaba da haska shirin ba, duba da wata matsala da aka samu da jarumar shirin Nafisa Abdullahi. Duk da dai su masu shirya shirin ba su bayyana hakan a matsayin dalili ba.
Sai dai cikin wani gajeren video da aka wallafa na daukar shirin ya nuna yadda ake daukar sabon shirin inda aka hangi fuskokin jaruman shirin ciki har da Fati Washa wacce kuma a baya babu ita wanda hakan ke nuna itace ta zama Sumayya.
Sai dai abin jira a gani shine Ko shirin zai dawo da armashin sa Kamar yadda aka saba a baya? Kuma ita jaruma fati washa za ta iya maye gurbin Sumayya a cikin wannan shirin?
Wasu na tunanin cewa Fati Washa ba ta da salo irin na Nafisa hakan yasa shirin ba zai yi armashi ba. Amma dai wasu na ganin Fati za ta yi fiye da Nafisa. Lokaci ne dai kadai zai nuna hakan.
Ga kadan daga bidiyon da mai bada umarni Aminu Saira ya wallafa