Babu abinda yakai auren soyayya daɗi da annashuwa. Indai akwai soyayya tsakanin to akwai farin ciki. Shiyasa auren dole ya zama tsohon yayi a wannan zamanin.
Jaruma Ummi Rahab ita da angonta Lilin Baba sun fitar da wasu hotuna na yiwa Yan uwa da abokan arziki murnar Barka da Sallah. Wanda hotunan suka ja hankalin mutane musamman a kafafen sadarwa na zamani.
Kai daga ganin hotunan ba sai anyi maka wani dogon zance ba kasan cewa akwai soyayya mai karfi a tsakanin su. Wannan ke nuna cewa auren soyayya suka yi da juna.
Wani abin birgewa kuma shine yadda cikin ƙaramin lokaci ma'auratan suka canja suka yi kyau da kuma kara kiba, Masha Allah. Allah ya kara Soyayya. Allah ya haɗa kan ma'aurata a duk inda suke.