Asirin wata Yarinya ya tonu bayan tayi yunkurin damfarar Mahaifinta kudi a Zaria


Daya daga cikin daliban makarantar mata na Dogon Bauchi dake sabon garin Zariya ya tonu, dalibar dai ta kasance cikin rukunin daruruwan daliban da Gwamnatin Jihar Kaduna ta Biyawa jarabawan NECO a banan nan cikin wannan makaranta."


"Sai dai daliban taje gida, bisani take Sanar da Mahaifinta cewa! ance a makarantansu kowata daliban da gwamnti ta Biya mata kudin jarabawan NECO ta kawo Dubu shida (6,000). 


"Mahaifin yarinyan me zai yi inba fadaba, na ganin cewa ai gwamnatin Jihar Kaduna ta biyawa yarinyarshi kudin jarabawan NECO, toh" wani kudi kuma za'a kara biya har dubu 6,000!


"Majiyar ya shaida mana cewa, Mahaifin yarinyan bai yi kasa a gwiwaba sai ya taso keyar yarinyan nashi zuwa makarantan a domin jin dalilin dazai sa ace a kawo kudi har dubu 6,000, 


"Sakamakon hakan; hukumar makarantan Matan na dogon bauchi dake sabon garin zariya ta karyata wannan batu na cewa hukumar makaranta tace kowata daliba takawo dubu 6,000.


"Mahaifinta daliban ya umarci da hukumar makaranta tayi hukunci akan yarinyar tashi. Hukumar makarantan dai ta dauki salon hukunci na biyan tara ga sauran dalibai a domin wannan ha'inci da daliban tayi yunkurin yiwa mahaifinta ya zama izna ga sauran dalibai tare da yi mata wasu bulalai masu ratsa jiki."

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post