Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ga Tawagar Shugaba Buhari A Kan Hanyar Zuwa Daura


Yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Yammacin Talatar nan a hanyarsu ta zuwa garin Daura da ke Jihar Katsina.


Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mallam Garba Shehu ya fitar, ta ce ’yan bindigar sun kai hari kan ayarin motocin ne dauke da jami’an tsaro da sauran hadimai a shirye-shiryen da shugaban kasar ke yi na tafiya Daura domin bikin Babbar Sallah.


Malam Shehu ya ce ’yan bindigar da suka yi wa ayarin motocin kwanton bauna, sun fuskanci tirjiya daga jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ’yan sanda da kuma DSS wadanda suka mayar musu da martani.


Sanarwar ta ce biyu daga cikin ya tawagar na karbar magani a sakamakon wasu kananan raunuka da suka samu, inda dukkan sauran ma’aikata da hadiman shugaban kasar suka isa Daura cikin aminci.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post