Ƴan Ajin Su Buhari Da Suka Yi Makaranta Tare Sun kaimasa Ziyara A Daura Har Sun Yi Masa Kyauta


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba bakuncin 'yan ajinsu a gidansa dake Daura a jihar Katsina a cigaba da karbar baki da yake yi na bikin babbar sallah.



Kamar yadda Buhari Sallau, hadimin shugaban kasan ya bayyana, mutum 14 ne suka kai masa ziyarar, ciki har da wata mace daya, Hajiya Binta 'Yar Malele.


Ya kara da bayyana cewa, daya daga cikin 'yan ajinsu, Sanata Abba Ali ya gwangwaje shugaban kasan da kyautar girmamawa.


Ba wannan ne karo na farko ba da ƴan ajinsu Buhari suka fara kaimusu ziyara ba a duk sanda shugaban ya je garin su na Daura tun bayan zaman sa Shugaban Najeriya.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post