Babu Abinda yafi min dadi Sai Idan na tuna cewa Idan Na Mutu zan Hadu da Annabi S.A.W, inji Marigayi Nura Mustapha waye a wani rubutun posting da ya taba yi a shafin sa na sada zumunta na Instagram.
Innalillahi wainna ilaihirrajiun Fitaccen darakta a Masana’antar shirya Finafinan Hausa ta Kannywood, wanda shine mai bayar da umarni a shirin nan mai dogon zango na "Izzar So" Nura Mustapha Waye gabanin rasuwar sa yayi wata wallafa a shafinsa na Instagram inda ya bayyana cewa Babu abinda yafi mashi dadi a duniyar nan.
Sai idan ya tuna cewa idan yau Allah ya ɗauki ransa zai hadu da masoyin sa Annabi Muhammad SAW, a yanzu kuma da Allah ya dauki Rayuwar hakan ya matukar bawa mutane mamaki kasancewar lokacin da yayi maganar ba kowa ne ya ankara da hakan ba sai bayan rasuwar sa.
Nura Mustapha wanda ake yiwa laƙabi da Waye anyi masa shaida sosai wajen yin hakuri da zama da mutane lafiya da kuma shaidar riƙo da addini. Muna addu'ar Allah ya jiƙansa da rahama kuma yasa ya hadu da masoyin sa annabi Muhammad (SAW).