Za'a Kunna Karatun Malam Abduljabbar A gaban Kotu


A cigaba da shariar da ake yi tsakanin gwamnati jihar Kano da Malam Abduljabar Kabara a zaman kotun na wannan rana lauyan da kotu tayi umarni yazo domin kare Malam Abduljabar Kabara Barr Dalhatu Shehu Usman yazo gabanta harma ya amince da kareshi. 


Mai sharia Ibrahim Sarki Yola yayi umarni da a Kunna Kundin dake ɗauke da muryar karatun Malam Abduljabar Kabara Wanda akansa ake zarginsa yayin da malamin ya musanta dukkanin zarg-zargen.


Yanzu haka dai kotu tayi umarni a saka a gaban kowa dake harabar Kotun domin Jin cikaken karatun malamin da ake zarginsa akai hakan zai sa ayi adalci wajen yi masa hukuncin da ya dace dashi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post