Wasu Muhimman Abubuwa 5 Dake kawo ƙarshen Soyayya tsakanin masoya


Yau a cikin wannan rubutun insha Allah zakuji wasu muhimman abubuwa wanda masoya  suke aikatawa wanda kuma daga ƙarshe ake rabuwa da juna. Shiyasa muka kawo muku waɗannan abubuwan domin masoya su san su kuma su kauce aikata su. 


Ayayin da masoya ke son yin hira da juna, sau tari a lokacin haɗuwar ne ake samun ɓacin rai da ke kaiwa ga rabuwa saboda yadda suke ɓata rawar su da tsalle. Wasu maza da mata sun bayyana abubuwan da ke kawo hakan da ma waɗanda ba sa ƙauna masoyan su su yi a lokacin hira a tsakanin su.


Akwai abubuwa da dama masu tarin yawa, sai dai kuma a cikin wannan rubutun ba zamu iya samun damar kawo muku su duka ba sai dai wasu daga cikin su. Ga jerin biyar daga cikin su da masoyan da mukai hira dasu suka bayyana cewa suna iya kawo ƙarshen soyayyar su:


(1) Dogon Jira;

Galibin masoya ba sa son dogon jira idan suka je hira ko za'a zo musu hira, musamman idan a lokacin suna son gabatar da ɓakin su ga masoyan su. Wani lokaci tun kafin masoyan su yi ido huɗu da juna ɓacin rai ke bayyana daga wanda aka bari yana dogon jiran.


A zantawar da mukai da wani masani a wannan fagen, yace yawancin maza sun tsani dogon jira idan suka je zance wajen budurwa. Domin wannan daɗewar na ƙona masa zuciya koda a cikin farin ciki ya zo, domin wasu mazan na ganin hakan wulaƙanci ne. Sai mutum yazo ya shafe sama da minti 30 yana jiran budurwa amma ba ta fito ba.


Wata budurwar ta san cewa zai zo, maimakon ta shirya da wuri ta jira shi amma ba zata shirya ba har sai ta bari sai ya iso za ta fara shiryawa, wata ma a lokacin za ta shiga wanka kuma kafin ta fito sai ta ɗauki kusan minti 30. Sannan kuma idan ta fito daga wankan sai ta tsaya yin kwalliya da saka kaya wanda shima sai ta shafe kusan minti 20 kafin ta gama.


Sai ya gama ɓata lokacinsa idan yana da wani uzirin sai dai ya haƙura tunda ta riga ta ɓata masa lokaci da sauran abubuwan da ya tsara zaiyi a ranar. Wasu matan na ganin cewa yin hakan wani abin burgewa ne ko kuma cinyewa ne su bar namiji yana jiran su, wasu kuma rashin tsari ne da su, wanda hakan kan sa mazan yi musu ba daidai ba har ta kai ga su mazan ake dogon jira.


Amma yana da kyau su fahimci cewa masoyansu sun zo ne da alheri kuma sun cancanci mutuntawa. Akwai rashin sanin yin abinda yakamata anan, duk wanda ya sanar dake cewa zaizo wajen ki rana kaza akan lokaci kaza amma sai kaga wai baza su shirya ba su jira mai zuwan ba, sai bayan yace yazo sannan wai za ta fara shiri. Wannan yana ɗaya daga cikin abubuwan da maza suka tsana kuma hakan yana yawon kawo saɓani a tsakanin masoyan.


(2) Ciye-Ciye;

Duk da cewa ana ganin wayewa ce ko alamar sakin jiki da juna cin abu a wurin saurayi ko budurwa, wasu kuma na ganin cewa hakan rashin kamun kai ne. Wasu mazan sun tsani mace ta fito hira wurinsu tana taune-taune ko a lokacin da suke tare. Wata idan ta fara taune-taune yadda kasan akuya sai dai kaji bakin yana ta mosti.


Masanin ya ce, wata macen kafin ta fito zance daga gidan su tana taunar cingam ko wani abu makamancin haka, kuma maza da yawa sun tsani irin hakan, idan wani na son hakan to wani ai ba ya so, kuma hakan ma akwai rashin kamun kai domin babu yadda za'a ai mace wacce tasan mai take yi ta ringa aikata irin wannan, a nawa tunanin ma babu wanda zai so hakan.


(3) Rashin Magana;

Masanin ya ce, maza ba sa son su je zance kuna hira ki yi ta ce masa ‘uhmm’ ko a'a, ko kuma ina ji’, shi ma hakan maza da yawa basa so. Akwai matan da zakaga cewa su halittar su ce haka basu iya magana ba haka Allah ya halicce su, wasu kuwa kawai iskanci ne da iyayi, kuma duk wanda zakiwa hakan gaskiya ba lallai bane ya iya jurewa ba.


Shi namiji yana so ki buɗe baki ki yi masa magana kar ki ce ‘ai yin hakan zubar da aji ne, to ina maganar zubar da aji kina hira da wanda kikeso ko kuma wanda zaki aur, ai idan zaki tsaya jan aji to wallahi zai rabu dake ne ya samu wata. akwai abun da yin su ba zub da aji ba ne. Ita mace ba'a son mai rawar kai da surutu kuma ba'a son mai yin shiru wacce ba ta yin magana.


(4) Maimaita Zance;

Duk da cewa mace na son ganin saurayi ya zo wurinta sun yi hira, amma kuma akwai abun da ke gundurar su, saboda haka a riƙa canja salon hirar da ake yi. Wasu matan ba sa son wanda kullum sai ya zo hira da mai yawan maimaita magana ɗaya kullum. Wasu mazan sai kaga basa yin wata hira mai muhimmanci kawai sai dai suyi ta nanata abinda sukai a hirar farko.


Da yake bayyana mana cewa ba ta son saurayi mai yawan maimaita magana ɗaya kullum, Sadiya Abubakar ta ce mene ne amfanin “ka zo zance amma hirar da za ka yi mata ta wancan zuwan da ka yi ne? Ina ganin hakan bai dace ba domin babu macen da za ta so hakan, kuma duk wacce kake maimaitawa zance to duk son da take yi ma za taji ka gundure ta.


Don haka yana da kyau tun kafin ka je zance ka tsara irin abubuwan da za ka faɗawa mace, kuma ba ko wane irin zance mara amfani ba, hira wacce za ta amfane ku kai da ita shi ya kamata ku yi, amma ba zancen kasuwa ko zancen ƙwallon ƙafa ba, zance mai ma'ana kuma wanda za ta ƙaru ta samu ƙarin sani a rayuwar ta, hakan ne zai sa ta farin ciki, idan ka tafi ta riƙa tuna ka har ta yi mafarkin ka.


(5) Ɓarin Zance;

Kar ka je hira kama yi wa mace hirar abin da ba ta so ko bai shafe ta ba, musamman hirar kwallon ƙafa ko makamancin haka. Wasu daga cikin ƴan matan da muka tattauna da su sun bayyana cewa, “duk saurayin da ke yi wa mace hirar ƙwallo, to za ta tsani hirar, a wani lokaci har shi kansa saurayin. Domin ita tana ganin cewa me hirar ƙwallo zata amfane ta da shi.


Saboda haka, duk da cewa wasu matan su ma ƴan kwallon ne, to amma dai da yawancin mata ba sa buƙatar irin wannan hirar, kuma ai ba abin da ke tsakaninku ba ke nan. Sun fi son hira irin ta soyayya wacce za ta ƙara muku soyayya junan ku, hira ta ilimi wacce zasu ƙaru da abubuwan da ba su san su ba, to irin wannan hirar mata suke so da kuma hirar irin rayuwar da za kuyi a zamantakewar auren ku. Don haka yana da kyau maza su ringa tunanin da kuma sanin irin hirar da mata suke so kuyi musu idan kunje zance wajen su.


Wannan sune kaɗan daga cikin jerin abubuwan da zamu iya kawo muku wanda ke jawo mace taji tana son Kasancewa da kai, da kuma ƙauracewa abubuwan dake gundurar su. Idan ka fuskanci abubuwan da mace take so to ka gama da ita, amma idan katsaya kana shirme to zakaga tana ja baya dakai tana nuna ka ishe ta. Su mata suna son kulawa kuma suna son kalmomi irin na soyayya masu tayar da ƙauna.


A ƙarshe muna fatan cewa maza da su kansu matan zasu kula sosai akan abubuwan da ya dace su ringa yiwa junan su wanda zai Inganta rayuwar soyayyar su. Domin idan kuka fuskanci junan ku, kuma kuka gane kowa abinda yakeso to babu shakka zakuga rayuwar ku tayi kyau cikin annashuwa da farin ciki. Da fatan Allah yasa mudace amin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post