Hukumar ƴan sanda ta jihar Katsina ta cafke wani matashin almajiri da zargin yiwa mai ɗakin sa fyade a ƙauyen Jikamshi na ƙaramar hukumar Musawa. Matashin mai suna Bello Jume ɗan kimanin shekaru 20 yaiwa mata 3 fyaɗe a kauyen ciki har da matar ubangidan sa.
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar SP Gambo Isah a yayin da yake gabatar da wanda ake zargi da yin fyaɗen ga manema labarai, yace wanda ake zargin bayan ya samu nasarar aikata mummunar aika-aika yin zina da matan, ya kuma sace musu kudi da sauran kayayyakin amfanin su.
SP Gambo Isa ya kuma kara da cewa, “a ranar 31 ga Mayu, 2022, da misalin karfe 9:00 na dare, wadanda abin ya shafa ‘yan shekara 18 zuwa 25, dukkansu a kauyen Jikamshi, sun kai rahoto a ofishin ‘yan sanda na Musawa cewa a ranaku da lokaci daban-daban, wani Jume Bello mai shekaru 20 da abokan aikinsa sun shiga gidajensu sun kai musu hari da wuka, suka yi musu barazana, inda suka kwace musu abubuwanda da suka hada da kudadensu, wayar hannu, da kuma tilasta musu suka keta masu haddi.
Wanda ake zargin ya shaidawa Katsina Daily Post cewa, “a ranar ne maigidana ya umarce da in kirawo matarsa mai sayar da ruwa, bayan na dawo da yamma ne na aikata mata wannan mummunar aika-aika.
“Eh, tabbas na karbe mata 'yan kudadenta, da na sauran jama'a. Na yi amfani da wuka ne don tsoratar da su. Na kai daya daga cikinsu a bayan gida nayi zina da ita yayin da nayi da ragowar matan akan gadon aurensu.”
SP Gambo ya bayyana cewa idan sun gama tattara bayanai akan wanda ake zargi za su gurfanar dashi a gaban kotu domin yi masa hukuncin da ya dace dashi. Sannan kuma yai kira da magidanta da su ringa sanin irin almajiran da za su ringa shiga gidajen su.
Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta kama wani matashi dan shekara 20 mai suna Jume Bello da laifin yiwa matar ubangidansa da wasu mata biyu fyade a kauyen Jikamshi da ke karamar hukumar Musawa.