Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Slow ta sayi Sabuwar Mota bayan wata uku da Samun kyautar Naira miliyan 1 da tai daga Naziru Sarkin Waka.
Fati Slow ta bayyana siyan motar tata ne a shafin ta na Instagram inda jarumai maza da mata ciki harda su Ali Nuhu suka taya ta murna.
Idan baku manta ba a kwanakin baya ne Naziru Sarkin Waka ya bawa Fati Slow Naira Miliyan ɗaya domin ta fara sana'a bayan da ya fahimci tana fama da rashin kuɗi sakamakon faɗa masa maganganu marasa daɗi da tai.
A lokacin da ya bata kuɗin Fati tace tabbas talauci ne yasa ta furta masa magana amma bazata ƙara ba inda a take Sarkin Waka ya yafe mata, tare da bata kyautar Naira miliyan ɗaya domin taje tayi Sana'a.
Bayan da kuɗi yazo hannun ta Fati Slow ta kama sana'ar siyar da kayan sawa da sauran su, inda a cikin wata uku Allah ya sawa kasuwancin nata albarka har ta sayi Sabuwar Mota.
Fati slow dai tsohuwar Jaruma ce da ta daɗe a masana'antar Ƙannywood tsawon shekaru da suka gabata. Sai dai harynzu ba ta yi aure ba amma ta bayyana hakan da cewa lokaci ne.