Sarkin Musulmi ya bada umarnin fara duban watan Zul Hajji Tun Daga Ranar Laraba


Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Ƙasa, NSCIA, Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Zul-Hijja daga ranar Laraba.


Sultan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a birnin Sokoto a a ranar Talata, mai ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi, Sokoto.


“Ana sanar da al’ummar musulmi cewa ranar Laraba 29 ga watan Yuni daidai da 29 ga watan Zul-Qidah 1443AH ita ce ranar da za a duba jinjirin watan Zul-Hijjah 1443AH. Don haka, an buƙaci Musulmai da su fara duban jinjirin watan a ranar Laraba kuma su kai rahoto ga gunduma ko ƙauye mafi kusa don tuntuɓar Sarkin Musulmi," "in ji shi.


Sarkin Musulmi ya roki Allah da ya taimaki al’ummar Musulmi wajen gudanar da ayyukansu na addini.


Zul-Hijja shi ne wata na 12 kuma na karshe a cikin kalandar Musulunci da ake gudanar da aikin Hajji a cikinsa, da kuma idin layya.


Ita ma kasar Saudiyya ta sanar da fara duban watan na Zul Hajji tun daga ranar Talata.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post