Samari Ga Wasu Hanyoyin Da Zaku Iya Tinkarar Mace Idan Kun Haɗu Akan Hanya


Maza da dama musamman samari idan sunga mace a hanya kuma ta burge su ba kasafai suke iya tinkarar ta ba. Wasu dai matan ne ke yi musu kwarjini, wasu kuwa kawai suna tsoron idan sun yi magana baza'a saurare su ba.


Yiwa macen da ka gani kana so a hanya magana ba abune mai sauki ba. Wannan yasa wasu maza da dama suke rasa macen da suka gani a hanya sukaji ta musu suna sonta.


Wasu mazan kuwa sukan yi karfin hali su tinkari matan, amma bada sigar da ya dace ba, don haka kodai taƙi sauraren su ko kuma ta saurarensu amma su kasa samun shiga.


A darusan mu na baya mun kawo wasu hanyoyi da dabarun tinkarar mace, a wannan karon ma ga wasu dabarun nan domin shawo kan macen da ka ganta kana so kuma bakasan Inda take ba.


(1) Ka Tabbatar Kayi Shiga Mai Kyau;

Kamin ka tinkari macen da bata sanka ba ka tabbatar kayi shiga mai kyau yadda bazata raina ganinka ba. Tunda ba sanin ka tayi ba ko kai wanene ko Dan wanene, don haka shigar mutuncin da zaka yi shine zai karfafa mata gwaiwar tsayawa ta saurareka.


(2) Sallama;

Hanya ta farko da saurayi zai bi domin samun saurin jawo hankalin mace ta saurareka kuma bata sanka ba shine ta hanyar yi mata sallama.


Ganin yadda sallama yake da ƙarfi kuma da mahimmanci a tsakanin Musulmai, da Kuma wajabcin amsawa wanda aka yi masa idan yaji kuma yana cikin natsuwa yasa duk macen da ka yiwa sallama muddin tana da tarbiya na addini zata amsa maka wannan sallamar taka, da zaran kuma ta fahimci magana kake son yi da ita zata tsaya ta saurare ka.


(3) Sakin Fuska Tare Da Fara'a;

Fara'a da murmushi sune abinda ya kamata ka yiwa macen da kayi mata sallama kuma ta amsa maka a daidai lokacin da kake gaisawa da ita.


Wannan fara'ar da murmushin zai sa su aika mata saƙon abunda kake da niyyar yi idan mace mai wayo ce ita. Don haka daga wannan lokacin zaka fahimci idan za ta saurareka ko kuma zata baka  wani uzuri na rashin tsayawa.


(4) Roƙon Iri;

Idan zaka yi mata wata magana bayan sallama da Kuma gaisuwa, sai ka riƙa haɗawa da tambaya cikin magana. Sai kace mata (Don Allah ko zan iya samun lokacinki na mintuna 2 ko 3 tunda naga kina sauri) wannan zai sa ta fahimci cewa da mutum mai mutunci take tsaye ba ɗan tasha ba.


(5) Kalamai Masu Ratsa Jiki;

Ka saukar da muryarka ƙasa-ƙasa a lokacin da kake mata magana kuma cikin girmamawa tare da yi mata Kalamai masu daɗi wanda za su jawo ta tsaya ta saurare ka.


(6) Ka Kasance Mai Ƙan-Ƙan Da Kai;

Kada kace za ka tsaya gaf da gaf da ita a lokacin da kuke magana, ka bata tazara tamkar kana ƙyamar kusantar ta. Hakan zai tabbatar mata cewa da gaske ne kake magana ba da wata manufa ta daban ka zo ba.


(7) Kada Ka Nuna Zalamar Ka;

Idan kana magana da macen da baka santa ba batasanka ba a karon farko ka guji saka idanuwanka akan halittunta irinsu ƙirjinta idan mai yalwan kirjice, ko kuma ƙugunta idan mai girman kuturice ita. Kana magana ne kana haɗa Idanuwa da ita sannan kuma kana maida kanka ƙasa bayan kun haɗa Idanuwa, a hakan za a yi hira.


(8) Banda Doguwar Hira;

Kada ka kuskura ka ja ta da hira mai tsawo yadda har za ta gaji tace maka za ta tafi. Kayi magana da ita a taƙaice koda kuwa ka fahimci tana jin daɗin hiran taka ka katsai ka sallameta ta tafi.


(9) Kada Ka Yawaita Yin Tambayoyi;

Kada ka dameta da yawan tambayoyin da kasan ba za ta so amsasu nan take ba. Saurin tambayar lambar waya ga macen da ba ta sanka ba yanada haɗari. Haka kuma ƙoƙarin sani ko tana da manema a wannan tsayuwan duk ba tambayoyi bane da suka dace.


Abu mafi dacewa shine neman izinin ganinta a mutunce a gidansu ko kuma inda take ganin zata baka dama tunda wannan shine farkon haduwar taku. Tare da ƙoƙarin sanin inda take son ku haɗun.


(10) Yaba Kyaun Haliitar Ta;

Kada ka sake ku rabu da mace ko wacce iri ce ba ka yaba da kyaunta da kwalliyar ta ba. Haka nan idan wani salon ɗaurin ɗankwali ko ɗinki tayi ka kambamasu ka yaba musu ka nuna mata wannan shine karon farkon da ka taɓa ganin wata mace da shi.


Irin wadannan kalaman sunfi komai a wajen mace kuma sune zasu tsaya a ƙwaƙwalwar ta bayan ta tafi duk abunda ka fadamata kamin wannan kalmar duk zata manta dasu sai wannan da ka zugata dasu.


Waɗannan sune abubuwa masu mahimmanci a haɗuwar ku ta farko da macen da bakusan juna ba. Duk saurayin da zai bi wannan hanyoyin to tabbas zai samu karɓuwa a wajen duk wata mace da ya tunkara da bai santa ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post