Safaru Ta Bayyana Dalilan Da Suka Jawo Aka Daina Sakata A Shirin Kwana Casa'in
Tsohuwar jaruma a shirin nan mai farin jini na kwana Casa'in Safaru ta yi wani martani da ya keta hazo a shafukan sada zumunta. Safarau ta bayyana wasu dalilai da ya jawo aka daina saka ta a cikin shirin kwana Casa'in na Arewa 24.
Tace tabbas bidiyon tsiraicina ne da ya fita ya jawo a koreni daga cikin shirin film É—in Kwana Casa’in kuma ni ba Æ´ar Ƙannywood bace. Asalima KannyWood bata yimin komai ba, Inji Safara’u
Matashiyar wacce a halin yanzu ta koma yin wakoki da asalin sunan ta shine Safiya Yusuf da ake yi mata laÆ™abi da Safarau, ta bayyanawa duniya cewa tabbas lokacin da aka sami matasala bidiyon tsiraicinta ya bayyana a duniya shine musabbabin abinda yasa aka koreta daga Kwana Casa’i.
Inda ta bayyanan cewa ita kwata-kwata ba ƴar Kannywood bace. Don haka take kira da ƴan Ƙannywood da su ƙyaleta haka su bar cewa Ƙannywood ne ya jawo tayi suna a duniya.
Safaru ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da tayi a shafin ta na Tiktok. Inda mutane suka tisata a gaba da tambayoyi, wasu kuma su É“ata mata rai. Hakan yasa ta hau zage-zage cikin fushi a yaren turanci.
Tun bayan da tashar Arewa dake haska shirin kwana Casa'in ta daina saka Safarau a cikin shirin hakan ne yasa ake ganin ya fusata matashiyar É—aukar wata rayuwa wanda mutane ke ganin babu inda za ta kaita sai ga halaka.
Leave Comments
Post a Comment