Kin zuwan Jarumi adam a zango daurin auren Ummi Rahab ya tada kura matuka inda rahotanni dake yawo a kafar sadarwa ta zamani suka nuna cewa Adam na matukar kishi da wannan auren.
Sai dai tun bayan bayyanar soyayyar mawaki liliyn Baba da jaruma Ummi Rahab rahotanni suka ringa fitowa cewa jarumi zango na matukar son auren Ummi wacce ita kuma taki amincewa da soyayyar sa.
Wanda hakan ya jawo suka samu matsala a tsakanin su, har suka daina fitowa a film tare. Wannan tataburza dai ta jawo cece kuce matuka inda aka sha drama mai zafin gaske kan wannan lamarin sai dai kuma a halin yanzu dai tuni aka daura auren Ummi Rahab din da angonta Lilin baba.
Yayin daurin auren dai an hango jaruman kannywood da dama amma ba a hango uba gareta ta kannywood din ba wato Adam A Zango inda wannan ma ya jawo zazzafar magana a kannywood din.
Wasu na ganin cewa kamata yai ace Zango shine kan gaba wajen bukukuwan Ummi Rahab duba da shi din kamar uba yake a gareta domin shine ya raine ta a masana'antar Kannywood har tayi suna.
Sai dai wasu na kusa da Adam Zango ɗin sun bayyana dalilan da yasa ba'a ganshi a wajen bikin ba. Inda suka bayyana cewa Adam A zango din yayi tafiya ne zuwa kasar waje inda ya halarci wani taro a kasar dubai.