A cigaba da ayyukan da rundunar sojin Najeriya suke yi na dakile ayyukan ƴan bindiga a yankin arewa maso gabas, wannan makon ma sunyi wata nasara a ayyukan nasu inda wasu mayaƙan ISWAP suka miƙa wuya.
Rundunar sojin a wata sanarwa da ta fitar a shafin ta na facebook a ranar 29 ga watan June na shekarar 2022 ta bayyana cewa ta samu wata gagarumar nasara a jihar Borno.
A sanarwar tace kimanin mayaƙan ISWAP su 314 ne suka ajiye makaman su tare da miƙa wuya ga rundunar sojin a karamar hukumar Bama ta Jihar.
Baya ga haka kuma hukumar ta sanar da cewa ta kuɓutar da wasu manoma kimanin su 12 da aka yi ƙoƙarin yin garkuwa dasu.