Wasu daga cikin ƴan matan garin Chibok su 2 da sojin Najeriya suka ceto su daga hannun ƙungiyar Boko Haram da suka sace su har cikin makarantar su a shekarar 2014 sannan kuma suka yi musu auren dole.
Sojojin dai sun samu nasarar kuɓutar da matan a cikin jeji kowacce da karamin yaron da ta haifa wa ɗan Boko Haram. Haka kuma rundunar sojin Najeriya ta gano tsaffin dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok ta jihar Borno da ke cikin ƴan mata 276 da kungiyar Boko Haram ta kwashe shekaru takwas da suka gabata.
Jaridar RFI Hausa ta rawaito cewa, a yayin da yake gabatar da matan a Maiduguri, Manjo Janar Christopher Musa, wani babban jami'in sojin Najeriya ya ce a wurare dabam-dabam sojoji suka yi nasarar samun matan a makon da ya gabata.
Mary Dauda da sojojin suka gan ta a cikin daji ta ce kawo yanzu Boko Haram ta aura wa mambobinta sama da matan Chibok 20 da ta baro. Ta ce mayakan Boko Haram kan lakada musu duka idan ba su yi sallah ba. Ita kuma Hauwa Joseph ta ce dan Boko Haram din da ya aure ta ya mutu a yayin wani gumurzu da sojojin Najeriya. Ta ce bayan mutuwarsa mambobin kungiyar sun yi watsi da ita da karamin yaron da ta haifa.