Innalillahhi: Yadda Ƴan Bindiga Suk Kai Wa Maniyyata Aikin Hajji Hari A Jihar Sakkwato


Ƴan bindiga sun kai hari kan wani ayarin maniyyata Aikin Hajji da ke fitowa daga ƙaramar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato a ranar Litinin.


Maniyyatan dai na kan hanyarsu ce ta zuwa birnin Sakkwato, don shirin tashi zuwa kasa mai tsarki da misalin karfe 7:30 na safiyar Talata. Maharan dai sun kai farmakin ne kan ayarin a daidai dajin Gundumi, amma jami’an tsaro suka dakile yunkurin nasu.


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa wani mazaunin garin Isa, Malam Sirajo, ya shaida musu cewa maniyyatan sun kubuta daga harin ba tare da ko ciwo ba, yayin da aka dawo da wasu daga cikinsu Fadar Sarkin Gobir Isa.


Ya ce, “Sun kai wa ayarin farmaki ne lokacin da suke cikin rakiyar jami’an tsaro, inda suka yi musayar wuta na wasu ƴan mintuna.


“Mun gano cewa wasu daga cikin jami’an tsaron sun ji raunuka, amma ba zan iya tabbatar da hakan ba, inji Sirajo da yake bayyana wa Aminiya.


Shi ma Shugaban Hukumar Bayar da Tallafin Karo Karatu ta Jihar ta Sakkwato, Shehu Muhammad Dange, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba zai iya sanin ko an saci wasu daga cikinsu ba ko kuma a’a.


Sai dai Kakakin Gwamnan Jihar Aminu Waziri Tambuwal, wato Muhammad Bello ya tabbatar da kai harin, amma ya ce an ceto ilahirin maniyyatan ba tare da ko kwarzane ba.


A cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Litinin, kakakin ya ce, “Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Isah Bajini Galadanchi, ya ce dukkan maniyyatan da ƴan rakiyarsu sun isa birnin Sakkwato lami lafiya.


“Tuni dai jami’an gwamnati suka karbe su, kuma suna shirye-shiryen tashi zuwa kasa mai tsarki da safiyar Talata,” inji sanarwar.


Sai dai da gidan Jaridar ta Aminiya sun tuntuɓi Kakakin ƴan sandan Jihar ta Zamfara domin jin ƙarin bayani game da lamarin sai dai ASP Ahmad Rufa’i, ya ce ba su da masaniya a kan harin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post