Haɗakar Sojin Najeriya, Kamaru Da Chadi Sun Hallaka Ƴan Boko Haram Fiye Da 800 A Tafkin Chadi


Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito wani rahotan rundunar na cewar tsakanin ranar 28 ga watan Maris zuwa 4 ga watan Yuni, haɗin gwuiwan sojojin sun gudanar da samamen haɗin kai a Tsibirin dake Tafkin Chadin da kuma ƙauyukan sa inda suka kashe tarin mayaƙan Boko Haram da na ISWAP.


Jaridar RFI Hausa ta rawaito cewa, rahotan ya bayyana samun gagarumar nasara a cikin samamen da suka yi wanda ya kai ga hallaka mutane 805 da kuma ko lalata motocin su 44 da babura 22 da kuma tarin ƙanana da manyan makamai.


Sanarwar tace akalla sojoji 3,000 suka shiga aikin samamen ta kasa da ruwa da kuma sama wanda ya kunshi sojojin kasashen 4 na Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi inda suka kwashe kwanaki 45 suna yi.


Rahotan yace sojojin sun ƙwace tarin makamai da bama-bama bayan gano inda ake sarrafa su, yayin da wasu sojojin Nijar kusan 20 suka samu raunuka sakamakon tashin abin fashewar.


A baya-bayan nan dai haɗakar sojojin suna samun nasarar a harin da suke kaiwa ƴan tayarda ƙayar baya waɗanda suka addabi yankin Arewa maso gabas. Ko a watan da ya gabata sai da aka samu wasu dayawa daga cikin ƴan ta'adan sun ajiye makaman su.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post