Fiye Da Mutane Dubu Ne Suka Rasa Rayukansu A Dalilin Girgizar kasa A Afghanistan


Ana cigaba da aikin ceto a yankin Kudu maso gabashin Afghanistan bayan mummunar girgizar kasa da ta yi sanadiyar mutuwar mutun kimanin dubu da raunata wasu dubu da 500.


Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da kai kayayakin agaji da suka hada da abinci da maganguna a yankunan da iftila'in ya faru mai iyaka da kasar Pakistan.


Batun sake tsugunar da mutane da suka tsira da samar masu da ruwan sha a cikiin gaggawa na daga cikin muhimman bukatun da ke gaban kungiyoyin agaji a cewar Majalisar Dinkin Duniya.


Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka sun bayyana anniyarsu ta kai ɗaukin gaggawa ga al'ummar Afghanistan, bayan da suka nuna kaduwa kan mummunan girgizar kasar.


Wani mai suna Ramiz Alakbarov da ke yankin na kudancin Afghanistan, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar da akwai kimanin gidaje fiye da dubu biyu galibi wadanda aka gina da laka da suka ruguje, sakamakon girgizar kasar mai karfin maki "5,9".

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post