Bidiyo: Kimanin mutane dubu 5 ne suka samu tallafin kuɗi domin yin jari daga Ahmad Musa


Yadda ɗan kwallon ƙasa Ahmad Musa ya raba kuɗaɗe ga mata da maza a birnin Jos domin su yi jari. 


A ranar Lahadi ne dai gidan ɗan wasan Super Eagle Ahmad Musa yai cikar kwari da jama'a domin karɓar tallafin kuɗi da ya ringa rabawa al'ummar garin Jos domin su rage raɗaɗin rayuwa.


Cikin bidiyon da ke yawo a kafar sadarwa ta zamani anga yadda dandazon mutane suka cika gidan Ahmad Musa inda yake binsu ɗaya bayan ɗaya yana raba musu kuɗaɗe a cikin takardar envelope. Sai dai ba'a san adadin kuɗin da ya ringa bayarwa ba.


Baya ga dimbin mutanen da suke cikin gidan nasa suna karbar kuɗin an hangi wasu tarin mutane a wajen gidan waɗanda basu samu shiga ba suma suna jira a shigar dasu domin su karbi nasu tallafin.


Wannan dai bashi ne karo na farko ba da ake ganin ɗan wasan yana bada tallafin kuɗaɗe ga mabukata kama daga zuwa gidan yari asibitoci gidan marayu da sauran wurare da dama.




Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post