A ranar daya ga watan Yuli mai kamawa ce ake sa ranar da za'a ci gaba da haska fim ɗin shirin Labarina mai dogon zango wanda kamfanin Saira movies suke shiryawa.
Daraktan shirin, wanda Malam Aminu Saira ke ɗaukar nauyi, shine ya sanar da hakan. A sanarwar da ya fitar, daraktan ya ce,
“ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAH. Muna sanar da ma’abota kallon wannan shiri na Labarina mai dogon zango cewa insha Allah za mu cigaba da ɗaukar zango na biyar da na shida. Muna kuma sa ran fara haska muku shi a wata mai kamawa (JULY 2022) in sha Allah. Muna ba ku haƙurin akan dogon jira da kuka yi. Muna godiya ga ƙaunarku gare mu Allah Ya bar zumunci.”
Idan ba'a manta ba, an dakatar da shirin ne a zango na huɗu tun bayan daina ganin jaruma Nafisat Abdullahi, inda ta sanar da cewa ba za ta samu cigaba da fitowa a shirin ba, wanda wasu suke tunanin kamar matsala ce aka samu.
Sai dai yanzu shirin zai dawo, kuma ba tare da ita ba, wanda hakan ya sa masu kallo suke kwaɗayi domin ganin yadda za ta kaya.
Andaɗe dai ana ta cece kuce akan shirin film ɗin Labarina wanda aka ɗauki tsawon lokaci ba'a haskawa, wanda har wasu suke tunanin cewa ma andaina yin shirin tun bayan bayyana ficewar jaruma Nafisa Abdullahi daga cikin shirin.