Reshen ɗalibai na Gamayyar Ƙungiyoyin Farar hula na Arewa, CNG-SW sun yi barazanar rufe filayen jirgin sama da tashoshin jirgin ƙasa da manyan titunan na Arewa idan har gwamnatin tarayya da ASUU ba su sansata an janye yajin aikin da suke yi ba.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ɗaliban sun kuma yi barazanar rufe ofisoshin jam'iyyun siyasa a jihohi 19 na yankin Arewa a Nijeriya matuƙar ba'a dakata da yajin aikin na ASSU ba.
CNG-SW ta yi wannan barazana ne a wata takardar bayanin bayan taro, wanda koodinetocin kungiyar na jihohi 19 su ka gudanar a ranar Juma'a a Kano.
Da ya ke karanta takardar ga manema labarai, Koodinetan kungiyar na ƙasa, Jamilu Charanchi ya ce CNG-SW ta cika da damuwa bisa yadda yajin aikin ASUU da na kwalejojin ilimi ya ci tira. A cewar ƙungiyar yajin aikin ya jefa ƴaƴan talakawa cikin wata irin mawuyaciyar rayuwa.
CNG-SW ta ƙara da cewa tuni ta ɗauki gaɓaran rubuta ƙorafi ga sarakunan gargajiya, malaman addini, jami'an gwamnati da jami'an tsaro a kan su saka baki a kawo ƙarshen yajin aikin.
"Idan haka ba ta samu ba, to za mu rufe filayen jiragen sama da tashoshin jirgin ƙasa da manyan titunan Arewacin Nijeriya. Haka kuma za mu rufe ofisoshin jam'iyyun siyasa a jihohi 19 na yankin Arewa," in ji CNG-SW.
An shafe watanni dai ana gudanar da yajin aikin wanda har zuwa wannan lokacin aka kasa samun daidaito a tsakanin gwamnatin tarayya da malaman jami'a