AL'ADA: Wata Ƙabila Da Basa Auran Maza Sirara Sai Masu Ƙiba Da Girman Tumbi


kabilar Bodi, wata kabila ce wacce mata basa auran maza sirara sai masu kiba da katon tumbi. Iya girman tumbinka iya farin jininka a gun ƴan mata.


A yau cikin shirin namu munzo muku ne da labarin wata kabila da matan cikinta sunfi so da kaunar maza masu katon tumbi. Wannan ƙabilar ƴan mata basa sha'awar ganin maza sirara.


A tsarin kabilar Bodi dake kasar Ethiopia, mazaje masu katon tumbi sune wadanda mata suka fi rububin dauka kuma suka fi so da kauna.


Domin a kabilar iya girman tumbinka shine yake nuna irin farin jininka a tsakanin 'yan matan garin. Wannan yasa mazan garin suke bakin kokarinsu ganin sun karawa tumbinsu girma domin su samu yan matan da za suyi rububinsu.


Suna gauraya jini da madara, sannan su sha domin kara kiba da kuma kara girman tumbin nasu. 


'Yan Wannan kabila ta BODI suna zaune ne a wani dan karamin tsuburi da ake kira da Omo a kasar ta Ethiopia, kuma suna matukar alfahari da wannan al'ada tasu ta rainon tumbi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post