Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar Najeriya zai cigaba ne daga inda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya tsaya.
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Ahmad Lawan, wanda shima ɗan takarar shugabancin ƙasa ne a jam’iyar APC, ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da yake jawabi ga wakilan jam’iyyar APC a zaɓe fidda gwani na shugaban ƙasa da za a yi nan gaba a Dutse, jihar Jigawa.
“Duk da cewa gwamnati mai ci ta yi ayyuka da yawa ta fuskar kara habbaka tattalin arziki da samar da tsaro ga ‘yan kasa, amma dai akwai bukatar kara kaimi akan abubuwa da dama. Gwamnati ta kashe Kuɗaɗe masu yawa don haɓɓaka harkar tsaro amma haka ba ta cimma ruwa ba’, ba mu samu nasarar da ake buƙata ba, amma hakan ba yana nufin ba mu yi komai ba.
“Kimanin shekaru 23 da na yi a matsayin ɗan majalisa sun ƙara min fahimtar hakikanin al’amuran da suka shafi harkokin mulki a ƙasar nan.” cewar Ahmad Lawan.
Sai dai bayanan na Ahmad Lawan sun jawo cece-kuce ga al'ummar Najeriya inda wasu ke ganin cewa ba zaiyi nasara a zaɓen ba koda an tsayar dashi. Shi kansa Muhammad Buhari ƴan ƙasa na ganin cewa bai yi musu komai ba na cigaban rayuwa a tsawon shekaru 8 da ya shafe yana mulkin ƙasar.