Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya bada haƙuri ga iyaye da ƴan uwan waɗanda aka yi garkuwa dasu a jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, inda ya tabbatar da cewa suna yin aiki tuƙuru wajen dawo da ƴan uwansu gidajen su ba tare da samun wata matsala ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin da yake karɓar gaisuwar sallah a ranar Litinin a fadar gwamnatin dake Villa. Mai magana da yawun sa Femi Adesina a wata sanarwa da ya fitar. Yace shugaban ƙasa ya bayyana cewa ƴan bindigar suna amfani da mutanen da suka kama ne a matsayin wata garkuwa.
Ya ƙara da cewa a wannan lokacin da muke tsananin farin ciki a tsakanin abokai da iyalai, sai dai muna sane da cewa wasu iyalan suna cikin yanayi na tsoro da zaman ƙunci sakamakon rashin ƴan uwansu da ƴan bindiga suka yi garkuwa dasu.
Don haka muna ƙara kira da jami'an tsaro da su jajirce suyi gaggawar kuɓutar dasu daga hannun masu satar mutane cikin ƙoshin lafiya ba tare da wani ya samu wata matsala ba, inji shugaba Muhammad Buhari.