Yanzu-yanzu: Hukumar Shirya Jarabawar JAMB A Najeriya Ta Saki Sakamako - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Yanzu-yanzu: Hukumar Shirya Jarabawar JAMB A Najeriya Ta Saki Sakamako


Hukumar dake shirya jarabawar shiga jami'a a Najeriya da akafi sani da JAMB ta sanar da fitar da sakamakon Jarabawar da ɗalibai suka zana a bana a faɗin ƙasa.


Fabian Benjamin shine shugaban sashen hulÉ—a da jama'a na hukumar ta JAMB, shine ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Asabar, inji rahoton Jaridar The Nation. Inda ya bayyana cewa É—aliban da suka samu zana jarabawar za su iya duba sakamakon su ta wayoyinsu na salulu.


"Don duba sakamakon UTME, kowane É—alibi da ya rubuta Jarabawar zai iya duba abinda ya samu ta wannan hanyar kamar haka: tura UTMERESULT zuwa 55019 da lambar wayar da akayi amfani wajen rijista, za'a turo musu sakamakon su kai tsaye."


"Wannan shine hanya daya tilo da aka samar don duba sakamakon a yanzu don wasu dalilai." Don haka duk É—alibin da yasan cewa ya zana jarabawar JAMB to yai gaggawar duba sakamakon sa.

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel