Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya lashe zaɓen fidda gwanin yan takaran shugaban ƙasa a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party PDP.
Jaridar legit Hausa ta rawaito cewa, bayan shafe sa'oi sama da 15 dalaget suka taru a filin wasa na babban birnin tarayyar Abuja, an Sanar da ƙuri'un da kowane mai neman takara ya samu.
Rahoton ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya samu nasara da ƙuri'u masu rinjaye akan gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike.
Kamar yadda yayi a 2019, Atiku yanzu shine zai wakilci jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa da za'a gudanar a shekarar 2023.
Atiku ya lallasa yan takara 12 da suka fafata a zaben inda ya samu kuri'u 371 Wanda ya zo na biyu shine Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike wanda ya samu kuri'u 237. Sannan Bukola Saraki wanda ya samu kuri'u 70.