Yadda ake gane masoyin gaskiya da mayaudari


Muddin namiji ko mace ba za su iya bambance tsakanin masoya na gaskiya da na ƙarya ba, a kullum zasu riƙa faɗawa cikin matsaloli na soyayya. 


Akwai masoya da suke yin soyayya ba tare da sun tabbatar da irin son da suke yiwa junan su ba. Wasu na yin soyyaya ne saboda wasu dalilai wanda ba za su kai ga aure ba. Shiyasa a yau muka kawo muku wasu hanyoyi da za ku gane masoyan gaskiya da na ƙarya.


Ga wasu hanyoyin da maza da mata za su iya bambance masoya na gaskiya da na ƙarya. Duk da darasin yafi karkata ne ga mata. Amma akwai wasu alamomin da maza ma za su iya amfani dasu.


(1) Masoyina na gaskiya yana iya yin komai akan ka domin ganin ya biya maka buƙatar ka.

Amma shi mai soyayya na ƙarya kansa kawai ya sani. Duk wani abu na matsala idan ya taso baza a ganshi ba sai abun ya wuce.


(2) Shi mai son ki da gaske ba zai taba furta miki kalamai na ƙarya ko na yaudara ba koda wasa ne. Amma shi maƙaryacin masoyi bashi da abun faɗi sai na ƙarya da yaudara.


(3) Duk wani mai son ki na gaskiya zai riƙa tausaya miki. Amma shi maƙaryacin masoyi bashi da wani aiki sai gallazamiki da ƙuntata miki.


(4) Duk wani mai son ka zaka same shi yana da haƙuri kuma yana maka uzuri. Amma shi maƙaryacin masoyi komai nasa na fushi ne da ɓata rai da son ayi faɗa da juna.


(5) Idan namiji na son ki kwantar da kansa ƙasa yake yi komai matsayinsa da girmansa. Amma shi maƙaryacin masoyi gadara, taƙama da nuna miki isa sune ɗabi'un sa.


(6) Ita macen da ta ke son namiji da gaske zaka sameta da yaba kyauta komai ƙanƙantar sa. Amma macen da son ƙarya take maka, duk abunda zaka mata sai ta raina ga rashin godiya.


(7) Idan namiji na son ki da gaske zai riƙa girmamaki da mutuntaki. Amma shi masoyin ƙarya baya ganin darajarki da mutunci a sarari da boye.


(8) Idan yana miki so na gaskiya zayi ƙoƙarin kare mutuncinki ne a duk inda ya kama. Amma idan soyayyar ƙaryar ce sune ma zasu soma jawo zancen da za a cimaka mutuncin.


(9) Idan mace tana maka so na gaskiya cikin ƙaramin lokaci zata yi ƙoƙarin ganin ta fahimceka. Amma ita wacce bata maka so na gaskiya ko lambar wayarka bazata iya kawowa a kanta ba bare ta fahimci wasu halayen ka.


(10) Duk wani mai son ki na gaskiya bazai taɓa nuna miki rashin yarda ba ko zarginki. Amma namijin dake miki ƙaryar so a kullum cikin rashin yarda dake yake saboda yawan zarginki.

 

Waɗannan sune kaɗan daga cikin wasu alamun da mata da maza da suke soyayya zasu iya tantance mai so na gaskiya da na ƙarya. Haka nan masu son ka a zahiri na rayuwa da masu cewa suna sonka a baka(baki).

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post