A ranar Litinin ne labari a Najeriya ya ɗauki hankalin al'umma game da siyan form da ƙungiyar Fulani wacce aka fi sani da "Miyatti Allah" suka haɗa maƙudan kuɗaɗe har Naira miliyan 100 suka sayi form ga tsohon shugaban ƙasa Dr Goodluck Ebele Jonathan domin ya sake fitowa yin takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2023.
Sai dai wasu rahotanni na bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya sayi form ɗin ne da kuɗin sa, domin yin takarar shugaban ƙasa ƙarkashin inuwar jam'iyyar APC, duba da kiraye-kirayen da al'umma da wasu ƙungiyoyi suke yi masa tun a watannin baya.
Sai dai kuma daga bisani anga wasu hotuna na tsohon shugaban ƙasa Goodluck tare da wasu daga cikin ƴan ƙungiyar Miyatti Allah cikin shigar Fulani suna miƙa takardun sayen form ɗin takarar ga Goodluck Jonathan wanda hakan ke tabbatar da cewa sune suka siya masa Form ɗin.