Ƙungiyar malaman jamia ta Najeriya ASUU ta bayyana tsawaita yajin aikinta da makonni 12 daga ranar Litinin 9 ga watan Mayun 2022. Emmanuel Asodeke, wanda shine Shugaban ƙungiyar ta ASSU ya sanar da cigaba da yajin aikin a wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar.
Emmanuel yace ƙungiyar ta ɗauki matakin ne bayan da Kwamitin Zartarwa ya yi wani taron gaggawa a sakatariyar ƙungiyar da ke Jami'ar Abuja. Ya ƙara da cewa bayan tattaunawa sosai da gwamnati akan yadda za'a kawo ƙarshen yajin aikin zuwa yanzu ta gano cewa gwamnati ta ƙi ɗaukar haƙƙoƙin da suka ratayu a wuyanta kan batutuwan da ƙungiyar ta bujiro da su a shekarar 2020.
Wannan dalilin ne ya sa muka ƙara tsawaita yajin aikin da mako 12 domin bai wa gwamnati lokaci don warware matsalolin da suke a ƙasa. Ya kuma ƙara da cewa ASUU ba ta ji daɗin yadda kwamitin da gwamnatin tarayya ta naɗa don warware matsalar ya nuna halin ko in kula kan batun ba, ta yadda ko sau ɗaya ba su kira su don ganawa ba.
Yajin aikin makaman jami'a a Najeriya dai ba sabon abu bane, domin an ɗauki tsawon lokaci ana yinsa, kuma harynzu ankasa samun daidaito tsakanin gwamnati da malaman jami'o'i. Sai dai wasu na kallon hakan a matsayin rashin ko inkula da gwamnatin ƙasar ke nunanwa.
Tunda yaransu ba'a ƙasar suke yin karatun su ba, Shiyasa basu damu suga cewa an daidaita wannan matsalar ba.