Biyo bayan wani rahoto da yake ta yawo a kafafen sada zumunta wanda ke nuna cewa tsohon shugaban Najeriya a jam'iyar PDP Dr Goodluck Jonathan ya sayi form zaiyi takarar shugaban ƙasa. Ƙarshe dai ya fito ya nesanta kan sa daga waɗanda suka ce sun saya masa fom domin tsayawa takarar shugaban ƙasar a zaben da za’ayi na 2023 a ƙarƙashin Jam’iyyar APC mai mulki.
Ikechukwu Eze wanda shine mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar a wata sanarwar da ya rabawa manema labarai tace Jonathan bashi da wata masaniya dangane da saya masa takardar takarar kuma bashi da wata alaƙa da waɗanda suke iƙirarin sun saya masa. Takardar sanarwar ta buƙaci Ƴan Najeriya da su yi watsi da rahotanni cewar zai tsaya takara a Jam’iyyar APC duk da yake sun san cewar wasu daga cikin kiraye-kirayen da ake yiwa tsohon shugaban na da matuƙar tasiri.
Idan ba’amanta ba wata kungiyar ƴan arewacin Najeriya da ake danganta ta da ta Fulani ta sanar da biyan Jam’iyyar APC naira miliyan 100 domin karɓar fom din takarar zaben shugaban ƙasar da sunan Goodluck Jonathan, matakin da ya haifar da cece kuce a ciki da wajen Najeriya.
Dama dai tun a watannin da suka gabata wasu ƙungiyoyin da magoya baya a Najeriya suke ta kiraye-kiraye da tsohon shugaban ƙasar kan ya fito ya tsaya takara domin ceto ƙasar daga halin da mulkin shugaban ƙasa mai ci Muhammad Buhari ya jefa ta. Sai dai ba'a ji tsohon shugaban ya amsa wannan kiran ba.